Isa ga babban shafi

WHO da UNICEF sun koka da yadda rabin asibitocin Duniya ke fama da rashin tsafta

Wani rahoton Majalisar dinkin Duniya ya koka da yadda rabin asibitocin Duniya suka gaza wajen wadata asibitocin da kayakin tsafta, dalilin da ya sanya mutane biliyan 4 fuskantar hadarin kamuwa da kwayoyin cuta.

Wani asibiti a nahiyar Afrika.
Wani asibiti a nahiyar Afrika. AFP - DANIEL BELOUMOU OLOMO
Talla

Wani rahoton hadin gwiwa tsakanin hukumar lafiya ta Duniya WHO da Asusun tallafawa kananan yara na UNICEF, ya ce galibin asibitocin basa tanadin tsaftataccen ruwan wanke hannu da sabulu ga marasa lafiyar da ke zuwa ganin likita da kuma a bandakun da ake shiga.

Rahoton ya ce mutane akalla biliyan 3 da miliyan dari 8 da 50 ciki har da marasa lafiya miliyan 688 basa zama ruwa da sabulun wanke hannu yayin hada hada a asibitoci     

Babbar jami’a a hukumar WHO Maria Neira ta ce abin takaici ne kuma sam baa bin lamunta ba ne barin asibitoci cikin kazanta da kuma rashin kayakin tsaftace wurare da jiki ga marasa lafiya da sauran masu ziyartar asibitocci.

A cewar jami’ar annobar corona ta bankado yadda asibitoci ke wasarere da kayakin tsafta hatta tsakanin jami’an lafiya

Maria Neira ta ce tsafta a cibiyoyin kiwon lafiya baza ta tabbata ba har sai an samu tsafatataccen ruwa da sabulu baya ga wanke bandakuna don kariya daga kamuwa da cutuka.

Rahoton na WHO da UNICEF da ya tattara bayanai daga kasashe 40 ya gano gazawar da ake fuskanta a cibiyoyin lafiya ta fuskar tsafta wanda ke haddasa asarar rayukan jarirai sabbin haihuwa akalla dubu kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.