Isa ga babban shafi

WHO ta yi gargadi kan yiwuwar cutar tarin fuka ta sake zamewa Duniya barazana

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce Cutar tarin fuka ko TB ta kama hanyar sake zama barazana a duniya, shekaru bayan raguwar karfin ta da aka gani, inda ta kashe kimanin mutane miliyan 1.6 a shekarar 2021 da ta gabata.

Wani likita yayin nazari kan hoton kirjin wani mai fama da cutar tarin fuka ko TB a asibitin dake yankin Gugulethu na birnin Cape Town a Afrika ta Kudu. 9/11/2007.
Wani likita yayin nazari kan hoton kirjin wani mai fama da cutar tarin fuka ko TB a asibitin dake yankin Gugulethu na birnin Cape Town a Afrika ta Kudu. 9/11/2007. AP - Karin Schermbrucker
Talla

Sabbin bayanan hukumar lafiyar ta duniya na ranar Alhamis sun nuna cewa yaduwar cutar tarin fukar ta karu da kashi 14 cikin dari  cikin shekaru biyu, inda ta kasha sama da mutane miliyan uku a shekarar 2020 da kuma 2021.

Bayan samun saukin cutar tun daga shekarar 2005, sai kuma ta fara tasiri kan majinyatarta da sabbin masu kamuwa da ita a shekarar 2019, inda ta yi sanadin hallakar mutane miliyan 1 da dubu 400, da kuma miliyan 1 da 500 a 2020 sai kuma miliyan 1 da 600 a shekarar 2021 da ta gabata.

WHO ta daura alhakin sake tsanantar cutar TB kan bullar annobar korona, saboda yadda ta karkata hankulan kasashen duniya kanta, inda al’umma ta gaza samun gwajin tarin TB ko maganinta.

Alkalumar Hukumar lafiya sun nuna cewa mafi yawan adadin wadanda cutar ta kashe an same su ne a kasashen Indiya da Indonesia da Myanmar da kuma Philippines.

Kashi biyu bisa uku na adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya: sun fito daga kasashen Indiya da Indonesia da China da Philippines da Pakistan da Najeriya da Bangladesh da kuma Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.