Isa ga babban shafi

Uganda ta sanar da kawo karshen annobar cutar Ebola a kasar

Uganda ta sanar da kawo karshen annobar cutar Ebola yau laraba, watanni 4 bayan bullarta wadda ta kashe mutane 55 a sassan kasar, matakin da ke zuwa bayan WHO da kanta ta sanar da shawo kan cutar.

A tsawon lokacin da Uganda ta yi fama da annobar ta Ebola an samu mutane 142 da suka harbu inda mutum 55 suka mutu yayinda 87 suka warke ciki har da kananan yara.
A tsawon lokacin da Uganda ta yi fama da annobar ta Ebola an samu mutane 142 da suka harbu inda mutum 55 suka mutu yayinda 87 suka warke ciki har da kananan yara. AP - Hajarah Nalwadda
Talla

Ministan lafiya na Uganda Jane Ruth Aceng a jawabinsa yayin taron bayyana kawo karshen cutar yau a yankin Mubende ya ce kasar ta yi nasarar shawo kan cutar wadda ta barke a watan Satumba.

Ita kanta hukumar lafiya ta Duniya, WHO ta tabbatar da nasarar kawo karshen cutar inda shugabanta Tedros Adhanom Ghebreyesus ke yabawa kokarin kasar ta gabashin Afrika game da matakan da ta dauka na gaggauta kawo karshen annobar cutar.

Yayin jawabinsa, minister Aceng ya ce yau 11 ga watan Janairu ake cika kwanaki 113 da bullar cutar wadda ta fantsama a sassan birnin Kampala said ai an gaggauta nasarar shawo kanta ta yadda yanzu haka babu ko mutum daya da ke dauke da cutar.

Karkashin dokokin hukumar lafiya ta Duniya dai idan har aka kwashe kwanaki 42 ba tare da samun sabon kamuwa da cutar Ebola a kasar da ake fama da annobarta ba, to kai tsaye an yi nasarar dakile yaduwarta.

A tsawon lokacin da Uganda ta yi fama da annobar ta Ebola an samu mutane 142 da suka harbu inda mutum 55 suka mutu yayinda 87 suka warke ciki har da kananan yara.

Cutar ta Ebola a wannan karon da aka bayyana ta da nau’in Sudan mai matukar hadari har zuwa yanzu babu rigakafinta ko da ya ke kamfanonin magunguna har guda 3 yanzu haka na aikin samar da rigakafinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.