Isa ga babban shafi

An samu rarar sama da dala biliyan 2 daga kudin tallafin corona

Hadakar shirin COVAX da ya tattara kudaden tallafawa kananun kasashe da kudaden samar da rigakafin covid-19 karkashin Gavi ta sanar da samun rarar dala biliyan 2 da miliyan 600 cikin kudaden da aka tara tun bayan barkewar annobar corona.

Hadakar shirin COVAX da ya tattara kudaden tallafawa kananun kasashe da kudaden samar da rigakafin covid-19 ya samun rarar dala biliyan 2 da miliyan 600.
Hadakar shirin COVAX da ya tattara kudaden tallafawa kananun kasashe da kudaden samar da rigakafin covid-19 ya samun rarar dala biliyan 2 da miliyan 600. REUTERS - TIKSA NEGERI
Talla

Hadakar shirin samar da alluran rigakafin na COVAX da aka yi hadin gwiwa tsakanin Gavi da hukumar lafiya ta duniya WHO sun bayyana shirin amfani da rarar kudin na dala biliyan 2 da miliyan 600 wajen kintsawa don zaman jiran ko ta kwana ta yadda kasashen Afrika za su iya samar da rigakafin duk wata annoba da za a iya fuskanta nan gaba a Duniya.

Wasu majiyoyi biyu da ke da kusanci da shirin na COVAX ya shaidawa Reuters cewa duk da yadda hadakar za ta ci gaba da aikin wadata kasashen Afrika da rigakafin na Covid-19 amma nan da zuwa karshen shekara za a karkatar da kudaden wajen samar da kamfanonin sarrafa magunguna da kuma zaman shirin ko ta kwana don tunkarar duk wata barazanar annoba da ka iya bulla a nan gaba.

Majiyoyin sun bayyana cewa an ware miliyan 600 daga kunshin kudin don zaman jiran ko ta kwana ko kuma yiwuwar sake waiwayowar annobar ta Covid-19 yayinda biliyan biyu kuma da aka karbo daga kamfanonin samar da rigakafin bayan cimma jituwa dawo da kudaden da aka biya su don samar da rigakafin a lokacin da cutar ta kai kololuwar tsanantarta.

A cewar majiyoyin za a yi amfani dala miliyan 700 wajen ci gaban samar da rigakafin a yanzu haka ga matalautan kasashe karkashin Gavi har zuwa shekarun 2024 da 2025 ko da ya ke kamfanin bai kai ga tsayar da magana da majalisar amintattunsa ba har sai bayan ganawarsu ta karshen makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.