Isa ga babban shafi

Yawan mutanen da Covid-19 ke kashewa ya ragu da kashi 95

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce adadin mutanen da cutar Covid-19 ke kashewa ya ragu da kashi 95 cikin 100 a shekarar bana, sai dai ta yi gargadin cewa har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa. 

Ma'aikatan lafiya yayin kulawa da wani mai  dauke da cutar Korona a Hong Kong.
Ma'aikatan lafiya yayin kulawa da wani mai dauke da cutar Korona a Hong Kong. REUTERS - TYRONE SIU
Talla

Hukumar lafiyar ta ce babu wani alamu da ke nuna za a iya kakkabe cutar baki daya daga doron duniya, kuma ya kamata jama’a su koyi yadda za su rayu da ita, da kuma irin sauye-sauyen da ta zo da shi. 

Shugabar kwamitin hukumar ta WHO da ke nazari kan yadda cutar ta yi tasiri Maria Van Kerkhove ta ce a halin da ake ciki yanzu kwayar cutar ta yi rauni sossai. 

Maria ta kuma kara da cewa a yanzu garkuwar jikin mutane ta fara yin kwarin da take iya bijirewa tasirin cutar Covid-19 din a jikinsu, sai dai duk da haka akwai bukatar a ci gaba da karbar allurar rigakafin. 

Don haka ne ta bukaci gwamnatocin kasashe da su ci gaba da zage damtse wajen bai wa jama’arsu igakafi da kuma yin gwaji da zarar an ga alamun cutar a jikin dan adam. 

Da yake jawabi, shugaban hukumar lafiyar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce har yanzu akwai kwarin gwiwar cewa cutar zata daina wani tasiri a jikin dana dam, amma dai akwai bukatar a kara zage damtse. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.