Isa ga babban shafi

Cutar diphtheria ta kashe akalla yara 30 a jihar Yoben Najeriya

Yara akalla 30 ne ake fargabar sun mutu, sakamakon kamuwa da cutar mashako ta Diphtheria, yayin da aka kebe 42 a cibiyar killace masu fama da cutar dake asibitin kwararru na karamar hukumar Potiskum a jihar Yoben Najeriya.

Wasu ma'aikatan jinya kenan da ke bawa yaran da ke fama da cutar Diphtheria kulawa a wani asibiti da ke kudancin Najeriya.
Wasu ma'aikatan jinya kenan da ke bawa yaran da ke fama da cutar Diphtheria kulawa a wani asibiti da ke kudancin Najeriya. © ET healthworld
Talla

Tandari, Misau, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Kasa, Boriya, Igwanda da Texaco sune wuraren da aka fi zargin wannan cuta ta fi yaduwa.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, majiya daga cibiyar killace masu fama da cutar, ya shaida cewa suna fama da karancin magunguna.

Ya zuwa yanzu dai a cewar majiyar, mutum 46 aka kwantar, inda mutum biyar daga cikin su suka mutu.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa, yara sama da 20 ne suka mutu a gida, yayin da kuma aka tabbatar da mutuwar hudu a asibiti, sakamakon wannan cuta.

Sai dai, jami’in da ke lura da cibiyar inganta ayyukan rigakafin ta karamar hukumar Potiskun, Mallam Buba, ya shaidawa Daily Trust cewa babu asarar rai da aka samu, amma akwai yara 42 da ke karbar kulawa a asibiti.

Ya kuma bayyana cewa, da dama daga cikin yaran da suka mutu, an gaza mika su asibiti ne akan lokaci.

Babban Daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko na Potiskun din, Mallam Abdurrahman Musa, la’akari da irin bayanan da suke samu game da yaduwar cutar ne, suka gudanar da aikin wayar da kan jama’a domin kaucewa yaduwar annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.