Isa ga babban shafi

Cutar mashako ta Diphtheria ta kashe mutane 80 a Najeriya- NDCD

Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC ta sanar da sake samun bullar cutar mashako ra Diphtheria a Abuja fadar gwamnatin kasar bayan da cutar ta kashe wani yaro dan shekaru 4 cikin watan yunin da ya gabata.

Wani yayin karbar rigakafi a jihar Kano ta Arewacin Najeriya.
Wani yayin karbar rigakafi a jihar Kano ta Arewacin Najeriya. NCDC TWITTER
Talla

Sanarwar da NCDC ta fitar a makon da muke ban kwana da shi ta ce daga watan Disamban barra zuwa yanzu na samu mutane 798 da suka harbu da cutar ta mashako cikin kananan hukumomi 33 da ke jihohi 8 da Abuja.

NCDC ta kuma bayyana cewa daga lokacin da aka samu bullar cutar ta farko zuwa yanzu na samu akalla mutane 80 da suka mutu sanadiyyar harbuwa da cutar a sassan Najeriya.

Cutar ta Diphtheria wadda ke da hadarin saurin yaduwa ta hanyar mu’amala da masu dauke da ita, ta kan tokare lumfashi tare da haddasa matsalar zuciyar, wanda ya fi tsananta ga kananan yara.

A cewar NCDC cutar ta fi tsananta a jihohin Kano wadda ta fi yawan masu dauke da ita kana Lagos sai Yobe da Katsina, sannan jihohin Cross River da Kaduna da kuma Osun.

Hukumar ta NCDC ta ce kashi 71.7 cikin dari na mutane dari 7 da 98 da suka harbu da cutar yara ne da shekarunsu ya farad aga 2 zuwa 14, lamarin da ke nuna hadarinta ga yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.