Isa ga babban shafi
Duniya

Ranar Ma’aikata: zanga zanga ta barke a wasu kasashen duniya

Kungiyoyin kwadago a kasashen Turai sun shirya gudanar da zanga-zangar adawa da matakan tsuke bakin aljuhun gwamnati domin gudanar da hutunsu na ma’aikata. Ma’aikata a Spain sun shiga zangar zangar ne saboda matsalar rashin aikin yi.

Wani Allo dauke da zanen Nicolas Sarkozy da Jam'iyyarsa a lokacin da ma'aikata suka fito zanga-zanga a birnin Lyon na Faransa
Wani Allo dauke da zanen Nicolas Sarkozy da Jam'iyyarsa a lokacin da ma'aikata suka fito zanga-zanga a birnin Lyon na Faransa REUTERS/Robert Pratta
Talla

A kasar Faran kungiyoyin kwadago sun shirya wata zanga zanga domin cin karo da yakin neman zaben shugaban kasa Nicolas Sarkozy wanda zai hada gangami a yau Talata.

Hankalin Faransawa zai rabu biyu domin wasu zasu bi tawagar yakin neman zaben Faransa wasu kuma zasu bi zanga-zangar ma’aikata da ke adawa da shugaban.

A Kasar Rasha, daruruwan magoya bayan shugaba Vladimir Putin ne suka hada gangami a birnin Moscow domin gudanar da bukin ranar Ma’aikata ana saura kwanaki a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 7 ga watan Mayu.

Irin wannan zanga-zangar ce ta barke a kasar Indonesia inda daruruwan ma’aikata suka fito domin neman karin kudaden albashi.

Mutane ne da dama suka fito a Jakarta dauke da tutoci masu neman karin albashi.

A Najeriya wasu kungiyoyin fararen hula a Birnin Legas sun yi kiran gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Shugaban kungiyar Kwadago a Najeriya yace ma’aikata a Najeriya suna cikin mawuyacin hali domin har yanzu akwai jahohin da basu amince da kudirin biyan ma'aikata karamin albashi N18,000.

A farkon shekarar nan ne gwamnatin Goodluck Jonathan a Najeriya ta jnaye tallafin Man Fetir wanda ya yi sanadiyar karin farashin mai daga N65 zuwa N97. An kwashe tsawon mako ana gudanar da zanga zangar adawa da Janye tallafin Mai a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.