Isa ga babban shafi
Wasanni

Dangantakar matasan Afrika da wasannin Turai

Wallafawa ranar:

Shirin Duniyar Wasanni ya diba gasar Premier ta Najeriya tare da tabo gasar league ta Orange a Jamhuriyyar Nijar. Amma shirin ya fi mayar da hankali ne akan tasirin wasannin kasashen Waje ga matasan Afrika musamman Najeirya da Nijar.

Wasu 'Yan Najeria suna kallon kwallon kasashen Turai a gidan kallon kwallo da ake biyan kudi a Legas
Wasu 'Yan Najeria suna kallon kwallon kasashen Turai a gidan kallon kwallo da ake biyan kudi a Legas Ahmed Jallanzo/roadto2010.com
Talla

A Najeriyar dai yawancin masoya kwallon kafa ba damuwa suka yi da gasar cikin gida ba, yawancinsu sun fi mayar da hanakali ne ga league league na Turai, musamman Premier ta Ingila ko kuma La liga a Spain ko Seria A ta Italia da gasar zakarun Turai da dai sauransu. Wannan kuma yana da nasaba da wasu matsaloli da ke tattare da league din na gida.

Kamar dai Najeriya, a Nijar ma yawancin matasan kasar hankalinsu ya fi karkata ne ga kallon wasannin Turai, kodayake akwai kishin goyon bayan kungiyar Jahata tsakanin Al’ummar Nijar. Amma duk da haka kungiyoyin Turai sun janye hanakilin wasu matasan.

Kodayake a Nijar yana da wahala ka ga ana kwallo tsakanin wata kungiya da wata kungiya ba ka ga an cika filayen wasa ba sabanin Najeriya. Domin ko wane dan Nijar yana fatar ace kungiyar Jahar shi ce ta kai ga nasara.

Shirin ya ji tabakin 'Yan Najeriya  da Nijar game da wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.