Isa ga babban shafi
Wasanni

Wasan Dambe a kasar Hausa

Wallafawa ranar:

Shirin duniyar wasannin yi yi bayani ne game da wasan Dambe a kasar Hausa da ke da tarihi mai tsawo. A zamanin dauri yawanci akan gudanar da wasan dambe ne tsakanin kabilubn hausawa daga yankunan kasar Hausa. Kuma ana gudanar da wasan ne yawanci a lokacin kaka. A can dauri akan shirya gasar Dambe domin maza su shirya zuwa yaki.

'Yan wasan Damben gargajiya a kasar Hausa
'Yan wasan Damben gargajiya a kasar Hausa
Talla

To sai dai a zamanin nan ‘Yan Dambe sukan gudanar da dambe a wani wuri da suka kebe da ake kira Gidan Dambe tare da makadansu da ke zuga su, kuma akan samu gidajen Dambe mafi yawanci a yankunan Arewacin Najeriya da kudancin Nijar da kuma Yankin Kudu maso Yammacin Chadi.

Amma shirin Duniyar wasanni ya kai ziyara ne a wani gidan Dambe da ke Unguwar Mile 12 Jahar Legas shiyar kudu maso yammacin Najeriya. Shirin ya zanta da 'Yan Dambe tare da tsokaci game da yadda ake yin Damben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.