Isa ga babban shafi
Boxing

‘Yan sandan Jamus sun saki Chisora bayan cafke shi

Bayan Cafke Dereck Chisora dan Dan Damben a kasar Jamus, yanzu haka ‘yan sandan kasar, sun sake shi ba tare da wata tuhuma ba bayan wani Damben bayan fage da suka yi tsakanin shi da David Haye na Birtaniya.

Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus
Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus REUTERS/Action Images/Andrew Couldridge
Talla

A jiya Lahadi ne ‘Yan sandan birnin Munich a kasar Jamus suka Cafke Chisora da mai bashi horo Don Charles, saboda Yunkurin da Chisora ya yi na abkawa Haye bayan ya sha kashi hannun Vitali Klitschko.

A ranar Assabar ne Vitali Klitschko ya doke Chisora a karawar ajin masu nauyi, amma an cafke shi ne a lokacin da ya ke shirin hawa jirgi zuwa Birtaniya.

Sai dai Yanzu haka ‘Yan sanda suna cigiyar Haye domin amsa tambayoyi

Ana zargin Chisora ne da kokarin abkawa Haye tare da yunkurin kai masa bugu.

Hukumar Damben Boxing ta Birtaniya tace zata kaddamar da bincike akan lamarin tsakanin ‘yan damben biyu, inda Chisora da aka cafke yace zai harbe Haye tare da kona shi.

Yanzu haka kuma shugaban hukumar Damben Boxin na kasar Jamus yace baya bukatar sake ganin Chisora a fagen Dambe a Jamus.

Haye dai dan damben Boxing ne kuma yana aiki ne da wata kafar Telebijin inda yake ta yayata cewa Chisora ya sha kashi a karawar shi da Vitali Klitschko, hakan ne kuma ya fusata Chisora.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.