Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Faransa ya ce wadanda suka sace bafaranshe a Katsina na da alaka da Alqa'ida

Francois Hollande wanda yake zantawa da gidan rediyon Europe 1 da ke kasar Faransa, ya ce ta la’akari da cewa mutane ne dauke da makamai suka sace bafaranshe bayan sun kashe wasu ‘yan Najeriya biyu, wata alama ce da ke kara nuni da cewa maharan na da alaka da kungiyar Aqmi wato reshen Alqa’ida a yankin Magreb da kuma Sahel.

Francis Colump Bafaranshen da aka sace a Jihar Katsina ta Najeriya
Francis Colump Bafaranshen da aka sace a Jihar Katsina ta Najeriya RFI Hausa/Tanko
Talla

Shugaban ya ce dole ne mu yi takatsantsan a game da duki wani batu da ya shafi ta’addanci, musamman ma a irin wannan lokaci da muke ci gaba tattaunawa domin ‘yantar da wasu Faransawa da aka sace.

A jiya alhamis ne dai wasu mutane dauke da makaman suka da aka ce yawansu yak ai 30, suka shiga cikin gidan wani injiniya bafaranshe a jihar Katsina a Najeriya inda suka yi awun gaba da shi bayan sun kashe wasu ‘yan Najeriya biyu wato daya mai kare lafiyarsa da kuma wani makwabcinsa.

Kasantuwar jihar ta Katsina a arewacin Najeriya inda ake da kungiyoyi masu kai hare-hare, da kuma halin da ake ciki a kasar Mali, wannan ya sa manazarta ke danganta wannan hari da kungiyar Alqa’aida a yankin na Magreb da kuma Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.