Harambee Stars na iya ba Super Eagles mamaki, inji Wanyama
Victor Wanyama Dan wasan kungiyar Celtic a Birtaniya ya ce Kenya na iya doke Najeriya a gobe Assabar wadanda za su kara a birnin Calabar a wasa neman shiga gasar cin kofin Duniya da a’a gudanar a Brazil a shekarar 2014.
Wallafawa ranar:
‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya suna da damar doke ‘yan wasan Harambee Stars na Kenya saboda dubban ‘yan kasar da za su shiga filin wasa domin mara masu baya.
Najeriya ce dai ke jagorancin rukuninsu da maki 4 bayan ta doke Namibia da ke a matsayi na biyu da maki 3. Kenya kuma tana matsayi na karshe ne kasan Malawi da zata kara da Namibia.
A birnin Ouagadougou kuma Burkina faso za ta karbi bakuncin Jamhuriyar Nijar
Congo kuma da ke jagorancin teburin rukuninsu da maki 6 za ta kai wa Gabon ziyaara ne wacce aka ragewa maki saboda ta yi amfani da dan wasan da be dace ba.
‘Yan wasan Eagles na Mali kuma za su kara ne da Rwanda yayin da kuma Sudan ta kece raini da Ghana.
A baya dai an datsewa Sudan yawan maki 3 saboda ta yi amfani da dan wasan da be dace ba a wasanta da Zambia. Kuma yanzu Zambia ce ke jagorancin Teburinsu na H da tazarar maki 6 tsakaninta da Ghana.
‘Yan wasan Elephant na Cote d’Voire kuma zasu kara ne da Gambia
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu