Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND ta dauki alhakin kisan ‘Yan sanda 15 a Niger Delta

A wata Sanarwa da kungiyar ta MEND masu ikirarin fafutukar 'yantar da yankin Niger Delta  ta rabawa manema labarai hadda Sashen Hausa na Radio Faransa, mai dauke sa hannun wani wanda kira kansa Jomo Gbomo, kungiyar ta dauki alhakin kai hari ga Jami’an tsaro wanda ya kashe akalla ‘Yan sanda 15.

Mayakan yankin Niger Delta (MEND) a Najeriya
Mayakan yankin Niger Delta (MEND) a Najeriya AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Sai dai kuma ‘Yan sandan Najeriya sun nisanta kungiyar MEND da alhakin kai hare hare wadanda suka ajiye makamai tun a shekarar 2009 karkashin afuwar da suka samu daga Tsohon shugaba Marigayi Ummaru Musa ‘Yar’Adua.

A Sanarwar da kungiyar ta aikawa kafafen yada labarai, kungiyar ta bayyana cewa da misalin karfe 5:00 na yamma ranar Assabar 6 ga watan Afrilu, Mayaka daga kungiyar fafutikar ‘yantar da yankin Niger Delta sun kai wa Jami’an tsaro farmaki tare da yin musayar wuta a Azazuma kudancin Ijaw a jahar Bayelsa.

A daya bangaren kuma Jami’an tsaro sun ce mayakan sun kai harin  kwantar-bauna ne tare da bude wuta ga ‘Yan sanda a Bayelsa wanda ya kashe ‘Yan sanda 12.

Wannan Harin na kungiyar MEND a Niger Delta na zuwa ne bayan mayakan sun aiko da sakon gargadin kaddamar da sabbin hare hare domin mayar da martani ga hukuncin da kotun Afrika ta Kudu ta yanke wa shugabansu Henry Okah.

Kungiyar ta MEND tace, tana fatan wannan fafatawar zata zama darasi da kuma gargadi ga jami’an tsaron tarayyar Najeriya, saboda kalaman da suke na tunzura jama’a.

A karshe kungiyar ta bukaci kanfanonin hako mai da sauran jama’ar da ke Niger Delta, da su yi watsi da tabbacin tsaron da Gwamnatin Najeriya ke ba su, da kuma kwantar da hankalin da wani mutum da ake kira Comrade Azizi ya yi da sunan kungiyar, suna masu cewa  su basu san shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.