Isa ga babban shafi
Wasanni

Kano Pillars sun lashe kofin Premier na Najeriya

Wallafawa ranar:

Shirin na Duniyar Wasanni ya yi bayani game da nasarar da Kano Pillars ta samu na kare kofinta na gasar Premier a Najeriya, Kuma Kungiyar ta lashe kofin ne karo na uku, kuma kungiya ta farko dagfa yankin arewacin Najeriya da ta lashe kofin sau biyu a jere bayan lashe kofin a bara.

'Yan wasan Kano Pillars suna murnar lashe kofin Premier na Najeriya karo na uku
'Yan wasan Kano Pillars suna murnar lashe kofin Premier na Najeriya karo na uku viakanopillars
Talla

Pillars sun lashe kofin ne duk da sun sha kashi a hannun Lobi Stars a wasan karshe da aka gudanar a ranar lahadin karshen makon shekaran jiya. Kuma Pillars sun samu nasarar ne bayan Bayelsa United da el Kanemi Warriors sun sha kashi a hannun Gombe United da Enugu Rangers ci 1-0.

Akwai kalubale da Pillars suka fuskanta musamman wasansu da Eyimba ta Aba da suka fafata har sau biyu bayan soke wasan farko. wasan Pillars da Eyimba an buga wasan ne ba tare da ‘yan kallo ba don gudun hatsaniya daga masoya kungiyoyin kwallon kafar guda biyu.

Kano Pillars ta lashe kofin ne da yawan maki 63, tazarar maki 1 kacal tsakaninta da Eyimba, Bayelsa United ce a matsayi na uku da yawan maki 61, sai El Kanemi a matsayi na hudu da yawan maki 60.

Kungiyar Enugu Rangers ce a matsayi na 5, sai warri Wolves a matsayi na 6, Gombe United ce kuma a matsayi 7.
kuma Alh Ibrahim Kwairanga shi ne Manajan Kungiyar Gombe United

Kungiyoyin da suka fice Premier ta Najeriya a bana sun hada da Kwara United da Bukola Saraki ABS da Wikki Tourist da kuma Shooting Stars.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.