Shirin Duniyar Wasanni ya tattauna ne game da nadin sabon kocin Super Eagles na Najeriya da kuma kalubalen da ke gabansa bayan hukumar NFF ta sallami Stephen Keshi.
A 16 ga wannan watan ne hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada Amodu Shuaibu a matsayin sabon mai horar da ‘Yan wasan Super Eagles bayan sallamar Stephen Keshi daga mukaminsa, bisa zargin gazawarsa wajan tafiyar da kungiyar yadda ya kamata musamman a gasar samun nasarar halartar gasar cin kofin Nahiyar Afrika da za’a gudanar a kasar Morocco shekara mai zuwa.
Shirin ya ji ta bakin ‘Yan Najeriya game da wannan sabon sauyin tare da tattaunawa da masana harakar kwallo a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu