Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe kusan mutane 40 a kauyukan Maiduguri

A Najeriya, wasu da ake zargi ‘yan bindiga sun hallaka kusa mutane 40, a kauyuka 5, dake kusa da Maidugrin jihar Borno, dake fama da tashe tashen hankulan masu alaka da kungiyar Boko Haram.

Wasu 'yan kungiyar Boko Haram
Wasu 'yan kungiyar Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun je kauyukan ne a kan babura da motoci, inda suka yi ta harbi cikin gidaje, tare da bindige wadanda suka yi yunkurin tserewa harin.
Wani matashi dan kungiyar Sintiri da ake kira Civilian JTF, mai suna Malum Idrissa, ya shaida wa kamfanin dillacin labaru na Reuters cewa hare haren sun auku ne a kauyukan da dake da nisa Mile 56 daga birnin Maiduguri.
Bayanai kan wannan sabon harin na zuwa ne kwana daya baya shugaban Najeriyan Muhammadu Buhari ya gana da takwarorinsa na yankin yammacin Africa, inda suka amince da kafa runduna ta musamman da zaya yaki ‘yan Boko Haram.
A makon da ya gabata hare haren bama bamai sun yi sanadiyyar kashe fiye da mutane 80 a birnin na Maiduguri.
Tuni shugaba Buhari ya umarci dakarun tsaron kasar su mayan da shalkwatar su zuwa birnin na Miaduguri, dake matsayin cibiyar ayyukan na Boko Haram.
Zuwa yanzu dubun dubatar muatane sun rasa ransu sakamakon rikicin na Boko Haram, yayinda wasu fiye da Miliyon daya da rabi suka tsere dag gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.