Isa ga babban shafi
Faransa-Najeriya

Buhari ya isa Faransa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Faransa a ziyarar aikin kwanaki uku da ya kai kasar, inda ake saran zai tattauna da shugaba Francois Hollande kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma yaki da kungiyar Boko Haram.

Shugaban Kasar Faransa  Francois Hollande Lokacin da ya ke tarba Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari a Elysee dake Paris
Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande Lokacin da ya ke tarba Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari a Elysee dake Paris REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Ziyarar ta shugaba Muhammadu Buhari wadda ita ce ta farko zuwa kasar tun bayan hawan sa karagar mulki, za ta bashi damar tattaunawa da shugaba Francois Hollande kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da suka kunshi harkar tsaro, kasuwanci da zuba Jari.

Faransa ta dade tana shirya taruruka tsakanin masu ruwa da tsaki kan yadda za’a murkushe kungiyar Boko Haram wadda ta taimaka wajen dai-daita yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya da wasu sassan Nijar, Kamaru da Chadi.

Shugaba Buhari zai gana da shugaba Francois Hollande da ministocin sa na harkokin waje Laurent Fabius da Jean Yves Le Drian na tsaro a yammacin yau, kana daga bisani zai gana da shugabanin kanfanonin da suka hada da na man Total, da kanfanin siminti Lafarge da kuma jakadun kasashen Afirka dake kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.