Isa ga babban shafi
Tanzania

An soke zaben yankin Zanzibar na kasar Tanzania

A kasar Tanzania al’umma sun soma bayyana shakkunsu dangane da sahihancin zaben kasar da ake jiran bayyana sakamakonsa a gobe alhamis, wannan dai ya biyo bayan soke zaben yankin tsibirin Zanzibar.

Tutar kasar Tanzania
Tutar kasar Tanzania
Talla

Shugaban Hukumar zabe na tsibirin Zanzibar Jesha Salim Jesha ya bukaci sake gudanar da zaben bayan zargin cewa akwai kurakurai da suka sabawa dokoki abinda yasa yace ya zama dole a soke zaben.

Wannan al’amarin na iya kawo jinkiri wajen bayyana sakamakon babban zaben kasar da al’umma ke dakon jin sakamakon a gobe .

Akalla mutane dubu dari biyar ne suka yi zabe a tsibirin Zanzibar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.