Isa ga babban shafi
Najeriya

Hallaka 'yan Shi'a rashin adalci ne- Human Rights Watch

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bayyana kisan da sojojin Najeriya suka yi wa daruruwan mabiya Shi’a a garin Zaria a matsayin rashin adalci.

Mabiya Shi'a  a lokacin gudanar da muzahara
Mabiya Shi'a a lokacin gudanar da muzahara AFP PHOTO PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A cikin wata sanawar da ta fitar a yau Laraba, kungiyar ta bukaci kwamitin bincike da gwamnatin Najeriya ta kafa da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya.

Human Rights Watch ta yi hira da mutane 16 da suka shaida aukuwar tarzomar tsakanin ‘yan Shi’a da sojojin kuma sun tabbatar ma ta cewa sojojin sun bude wuta a kan ‘yan Shi’a a wurare guda uku a Zaria.

Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta dauki matakin bude wutar ne bayan mabiya Shi’a sun yi yunkurin hallaka shugaban sojin kasar Laftanar Janar Tukur Buratai a lokacin da ayarin motocinsa ke neman hanyar wuce wa yayin da ‘yan Shi’an suka datse hanyar.

Daraktan Human Rights Watch a Afrika, Daniel Bekele ya ce, hukuncin da sojojin suka dauka ya yi tsauri kuma ya ce, dama an shirya kaddamar da farmaki kan ‘yan Shi’an.

A baangare guda, kwamitin tsaro na majalisar wakilan Najeriya ya yi ganawar sirri da Buratai a babban birnin Abuja, inda ya yi masa tambayoyi game da rikicin kamar yadda shugaban kwamitin Aminu Sani Jaji ya shaida wa manema labarai.

Jaji ya kra da cewa, nan gaba za su gayyaci Supeto Janar na ‘yan sandan kasar, Solomon Arase domin shi ma ya amsa tambayoyi.

A cewar jaji, tawagar da aka tasa zuwa Zaria domin jin ta bakin bangaren Shi’a ta dawo Abuja ba tare da yin nasara ba a bincikenta, amma ya bada tabbacin cewa kwamitin zai yi iya kokarinsa domin jin ta bakin ‘yan Shia’an.

A makon da ya gabata ne majalisar wakilan kasar ta bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin yayin da shugaban Majalisar Yakubu Dogara ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin cewa za a sanar da su sakamakon binciken.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.