Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Shi’a ta bijirewa zaman kwamitin bincike

Kungiyar Mabiya Shia a Najeriya ta ce ba za ta halarci zaman kwamitin binciken da gwamnatin Kaduna ta nada ba har sai an saki shugaban ta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Talla

Wata sanarwa da Ibrahim Musa mai Magana da ‘yan jaridu na kungiyar ya rabawa manema labarai, ta nuna cewar suna kuma bukatar sakin ‘yan kungiyar da aka tsare a gidan yari da barikin soji da kuma bada gawarwakin wadanda suka mutu dan yi musu jana’iza.

Kungiyar ta kuma yi korafi kan wasu daga cikin ‘yan kwamitin wadanda tace sun bayyana kiyayar su ga kungiyar karara kafin nada su a cikin kwamitin.

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin kasar ce ta kafa kwamitin na shari’a domin binciken rikicin da ya barke tsakanin shugaban sojin kasar, Laftanar Tukur Buratai da mabiya Shi’a a garin Zaria, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.