Isa ga babban shafi
Najeriya

Dan kunar bakin wake ya kashe mutane a Adamawa

Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu bayan wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa da bam a yau jumma’a a cikin kasuwar garin Gombi da ke jihar Adamawa na arewa maso gabashin Najeriya. 

Boko Haram sun sha kai hare hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya
Boko Haram sun sha kai hare hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya The Long War Journal
Talla

Rahotanni sun ce an kai harin ne a sashen sayar da hatsi da ke cikin kasuwar, kuma wanda ya kai harin yaro ne da bai wuce shakaru 12 da haihuwa ba.

Garin Gombi dai na da tazarar kilomita 120 daga babban birnin Yola na Adamawa kuma ya yi fama da hare haren kungiyar Boko Haram a baya.

Wannan dai na zuwa ne bayan wasu 'yan kunar bakin wake sun kashe akalla mutane 14 a ranar Larabar da ta gabata a garin Chibok da ke jihar Borno, inda mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata sama da 200 a watan Aprilun shekara ta 2014.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.