Isa ga babban shafi
Najeriya

Ese Oruru ta Bayelsa na dauke da juna biyu

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa, Ese Rita Oruru ‘yar shekara 14 da ake zargin wani matashi dan kano da sace ta, na dauke da cikin watanni 5 kamar yaddav wasu majiyoyi suka sanar.

Ese Oruru da ake zargin wani matashi dan Kano ya sace ta tare da yi mata ciki.
Ese Oruru da ake zargin wani matashi dan Kano ya sace ta tare da yi mata ciki. lucopros.info
Talla

An zargi Yunusa Dahiru da aka fi sani da suna Yellow da sace matashiyar daga jiharta ta asali wato Bayelsa, inda ya kai ta tasa jihar wato Kano.

Tuni dai Ese ta koma jiharta bayan an mika ta ga jami’an ‘yan sanda kuma a halin yanzu, tana nan zaune a wani ginin ‘yan sanda da ke birnin Yenagoa.

Mahaifin Yunusa dai, Dahiru Bala ya musanta cewa, dansa ya yi zaman daduro da yarinyar yayin da wasu majiyoyi ke cewa, za a tasa keyar Yellow zuwa Yenagoa domin fuskantar tuhuma akan zargin da ake yi masa na sace yarinyar da kuma tirsasa ma ta shiga addinin Islama.

Sai dai Ese ta musanta batun tirsasa ma ta karban wani addinin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.