Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo da ke tabbatar da cewa shugabanta Abubakar Shekau na raye. 

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.
Talla

An saba ganin Shekau a fayafayen bidiyon da ke nuna shi yana magana cikin baraza da kuzari, to sai dai sabon bidiyon na kusan minti takwas ya nuna shi a cikin wani yanayi da ke nuna cewa kungiyar ta Boko Haram na cikin wani hali na damuwa.

Shekau wanda ya yi magana da harshen Larabci da Hausa a cikin bidiyon ya ce,

Shi ne baban Muhammad, Abubakar dan Muhammad Shekau, jagoran kungiyar nan ta ma’abota sunna da ke yin kira tare da yin Jihadi. Sannan ya mika gaisuwa ga magoya bayansa tare da tunatar da su da su ji tsoron Allah.

Hotan bidiyon dai ya nuna Abubakar Shekau sanye da kakin soja da kuma rawani a kansa ga kuma bindiga a kafadarsa ta hagu, sannan kuma an jingine tutar Boko Haram a bangarensa na dama.

Ga dai cikakken rahoto tare da muryar Abubakar Shekau.

01:29

Muryar Abubakar Shekau na Boko Haram

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.