An samu gawar hafsan sojin da aka sace a Najeriya
Rundunar Sojin Najeriya ce ta sanar da labarin samun gawar kanar Samaila Inusa hafsan sojin nan da aka sace a karshen mako a yau talata da misalin karfe 6 na yamma.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sanarwar da rundunar sojan ta bayar ta hannun Daraktan yada labaran ta Kanar Sani Usman Kukasheka tace ana kyautata zaton an kashe hafsan ne ranar da aka sace shi, domin har gawarsa ta soma lalacewa.
Rundunar tace an samu gawar ce kusa da kauyen Ajyaita dake wajen jahar Kaduna.
Daraktan ya bayyana cewar rundunar sojin ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen zakulo wadanda suka kashe hafsan dan hukunta su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu