Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya jadada matsayinsa kan masu kai hari da sunan Makiyaya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jadada matsayin gwamnatin sa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar, inda ya ce ya baiwa jami’an tsaro umurnin kama wadanda ke kai hari da suna makiyaya da kuma tona musu asiri.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin ganawa da tawagar shugabanin mabiya darikar Katolika a karkashin shugaban su Rev. Ignatius Kaigama, Buhari ya ce a shirye yake ya samar da tsaro a kasar.

Shugaban ya kuma baiwa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan kasar da sauran Jami’an tsaro umurnin murkushe maharani.

Kana ya jajantawa shugaban mabiya darikar katolika dake Enugu da kuma mutanen Ukpabi Nimbo da sauran jama’ar Najeriya da suka fuskanci irin wannan hari.

A nasu bangare shugaban mabiya darikar katolikan sun shaidawa shugaban kasar cewar a shirye suke suyi aiki da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.