Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Mutane 17 sun mutu a fadan da aka yi tsakanin manoma da makiyaya

Wani fada da aka yi tsakanin manoma da Fulani makiyaya a garin Banou da ke arewa maso gabashin kasar Cote D’Ivoire ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 kamar dai yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara yana ziyarar inda aka kai hari a Grand Bassam.
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara yana ziyarar inda aka kai hari a Grand Bassam. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Ministan tsaron kasar Vincent Toh Bi ya ce an yi fadan ne tsakanin daren 23 zuwa 24 ga wannan wata na maris, ko baya ga mamatan, akwai wasu mutane akalla 39 da suka samu raunuka sakamakon sara ko kuma harbi da bindiga.

Har ila yau akwai jami’an tsaro biyar da suka samu raunuka a lokacin da suka je domin kwantar da rikicin. To sai dai ministan ya ce an tura jami’an tsaro kusan 900 domin dawo da zaman lafiya a yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.