Majalisar Dattawan Najeriya ta Gayyaci Ministan Sharia Abubakar Malami
Wakilan Majalisar Dattijan Najeriya sun umarci Ministan Sharia kuma Atoni Janar na kasar Abubakar Malami ya gurfana gaban Majalisar don yin bayani gameda zargin da ake yiwa Shugaban Majalisar Dattijan da Mataimakin sa na laifin sauya dokokin majalisa.
Wallafawa ranar:
Gayyatar Ministan na biyo bayan bukatar hakan ne daga Dan Majalisa Dino Melaye wanda yake cewa akwai matsala da ya hango dake neman yiwa tsarin Democradiyya lahani.
Wakilan majalisar Dattijai shida suka tofa albarkacin bakin su suna nuna goyon bayan su gameda bukatar gayyato Ministan Sharia yayi bayani.
Gwamnati na zargin Shugaban majalisar ne Bukola Saraki da mataimakin sa Ekweremadu da laifin sauya kundin tafiyar da harkokin majalisar don zaben da aka yi masu na Shugaba da mataimakin shugaban majalisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu