Isa ga babban shafi
Nigeria

Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai na Nigeria David Mark ya sake lashe zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria ta sanar da cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Sanata David Mark ya lashe sake zabe a mazabar sa ta Kudancin Benue wanda akayi  jiya Asabar.

Sabon shugaban jamiyyar adawa PDP a Nigeria Sanata Ali Modu Sheriff
Sabon shugaban jamiyyar adawa PDP a Nigeria Sanata Ali Modu Sheriff
Talla

David Mark ya sake tsayawa takaran karkashin jamiyyar sa ta adawa  PDP bayan rusa zaben sa da akayi kwanan baya.

Ya doke abokin takarar tasa Daniel Onjeh dan shekaru 41 da ya tsaya karkashin jamiyyar dake mulki yanzu APC.

A ranar 28 ga watan Maris daya gabata kotun koli dake Nigeria  ta soke zaben David Mark aka umarci Hukumar Zabe Mai Zaman kanta da ta sake zaben a mazabarsa.

Bayan zaben David Mark ya sami yawan kuri'u 84,192 , yayin da abokin takaran nasa ke da yawan kuriu 71,621.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.