Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana takaddama kan halattaccen gwamna a Abia

Gwamnatin Abia da ke Najeriya ta musanta ikirarin hukumar zaben kasar na cewa, gwamnan jihar Okezie Ikpeazu bai sanar da ita cewa zai daukaka kara game da hukuncin dakatar da shi da wata kotu ya yanke masa ba.

Uche Ogah da Okezie Ikpeazu da ke takaddama kan kujerar jihar gwamnan Abia da ke Najeriya
Uche Ogah da Okezie Ikpeazu da ke takaddama kan kujerar jihar gwamnan Abia da ke Najeriya thefocusng.com
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar a cikin daren daya gabata, gwamnatin ta ce, Mr. Ikpeazu ya sanar da hukumar INEC matsayinsa na daukaka karar don kalubalantar hukuncin, inda ta bayyana Saleh Ibrahim na sashen kula da shari’a a INEC a matsayin jami’in da ya karbi takardar Ikpeazu.

Sanarwar ta kara da cewa, da misalin karfe 12:50 na rana agogon kasar kuma a ranar laraba 29 ga watan Yuli ne, Saleh Ibrahim ya rattaba hannu kan takardar.

Sai dai Nick Dazan mai magana da yawun INEC ya ce, gwamnan ya yi kuskure da ya ajiye takardarsa a sashen na kula da shari’a inda ya ce, duk wata wasika ana mika ta ofishin shugaban hukumar ne kuma daga nan ne ake isar da ita inda ta dace.

Hukumar dai ta ayyana Mr. Samson Ogah a matsayin sabon gwamnan jihar bayan da ta mika masa takardar shaida, abinda ya haifar da takardama tsakanin mutanen biyu, inda kowanne ke kallon kansa a matsayin halattaccen gwamnan duk da dai kotun jihar ta dakatar da rantsar da Mr. Ogah wanda ya yi zaton zai sha rantsuwar kama aiki a yau jumma’a

Da farko dai Kotu ta dakatar da Mr. Ikpeazu ne bayan ta same shi da laifi mai nasaba da kaucewa biyan haraji.

Mr. Ogah shi ne mutumin da ya kalubalanci Ipeazu a zaben fidda gwani da jam’iyyar PDP ta gudanar a shekara ta 2014 kuma shi ne ya yi na biyu a lokacin, abinda ya sa ya cancanci maye gurbin Ikpeazu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.