Isa ga babban shafi
Najeriya

Motocin gwamnati dauke da abincin agaji sun bata a Maiduguri

Rahotanni daga garin Maiduguri sun nuna cewar manyan motoci 60 dake dauke da kayan abinci da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tura dan kai dauki sun bata, babu wanda ya san inda suka shiga.

Yunwa ya addabi 'yan gudun hijira a sansanonin su dake Maiduguri
Yunwa ya addabi 'yan gudun hijira a sansanonin su dake Maiduguri STRINGER / AFP
Talla

Dan Majalisar Dattawa Ali Ndume dake bayyana wa RFI hausa lamarin ya ce sun gano haka ne lokacin da suka zo raba abincin ga talakawa dake cikin matsanancin yunwa.

A cewar Ndume motoci 113 shugaba Buhari ya bayar da umarni akai jihar Borno, sai dai abin mamaki sai gashi 53 kawai suka iske.

Ndume ya ce tuni suka dakatar da raba abinci tare da sanarwa fadar Shugaban kasa halin da ake ciki, kuma yanzu haka Hukumar EFCC ta cafke wanda aka baiwa kwangilar jigilar abinci domin aiwatar da bincike.

Wanna al'amari na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya da kuma wasu hukumomin agajin na duniya ke ci gaba da janyo hankalin kasashen duniya kan tsananin yunwa da rashin abincin da ya addabi Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya da ya yi fama da matsalar kungiyar Boko haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.