Boko Haram: Yara 50,000 na iya mutuwa saboda Yunwa a bana
An bukaci gwamnatin Najeriya ta kara daukar matakan magance matsalar karancin abinci tsakanin dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara kanana kimanin 50,000 za su iya mutuwa a bana idan har ba gaggauta daukar matakan wadata su da abinci ba.
Kungiyar likitocin Doctors Without Borders tace akalla mutane 188 suka mutu tsakanin 23 ga watan Mayu zuwa 22 ga Yuni, sakamakon rashin abinci mai gina jiki.
Akwai tawagar gwamnati da ta kai ziyara sansanin ‘Yan gudun hijira a Bama domin ganin irin halin da ‘yan gudun hijira suke ciki, kafin bayar da tallafi daga gwamnatin Tarayya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu