Isa ga babban shafi
Najeriya

Fargabar ambaliyar ruwa a wasu Jihohin Najeriya

Hukumar kula da hasashen yanayi ta tarayyar Najeriya ta yi gargadin cewa jihohi 13 a fadin kasar na iya fuskantar ambaliyar ruwa, ciki harda kauyuka 50 a jihar Kwara.

Ambaliyar ruwa a Najeriya
Ambaliyar ruwa a Najeriya Reuters/路透社
Talla

Hakan yasa gwamnatin jihar ta Kwara kaddamar da shirin wayar da kan al’umma da kuma kwashe wadanda ambaliyar ka’iya shafa zuwa wuraren da zasu kauce wa hakan, kamar yadda mai bawa gwamnan jihar shawara kan muhalli Manzuma Kawu ya bayyanawa manema labarai.

Da yawa daga cikin kauyakun dake fuskantar barzanar na cikin kananan hukumomin Patigi, Moro da kuma Edu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.