Isa ga babban shafi
Najeriya

Jagoran Biafra zai kawo karshen gwagwarmaya

Jagoran masu neman samun ‘yancin yankin Biafra a Najeriya, Nnamdi Kanu ya ce a shirye ya ke, ya tattauna da gwamnatin kasar don kawo karshen gwagwarmayar neman samun ‘yancin kan yankin da ya ke. 

Jagoran neman yankin Biafra Nnamdi Kanu
Jagoran neman yankin Biafra Nnamdi Kanu REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kanu ya kuma yi tir da ayyukan tsagerun Niger Delta da nisanta mutanensa da ayyukan tsagerun.

Tun a watan Octoban shekara ta 2015 ne, jami’an tsaron Najeriya suka kame Nnamdi Kanu bisa zarginsa da cin amanar kasa.

Lauyoyin Nnamdi Kanu Ifeanyi Ejiofor da kuma Amoebi Nzelu, sun ce suna goyon bayan tayin wannan tattaunawa da jagoran Biafran ya yiwa gwamnatin Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.