Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane da dama ne suka mutu a tarzomar fafutukar kafa kasar Biafra

Hukumomin ‘yan sanda a Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 10 ciki har da ‘yan sanda biyu sakamakon tarzomar da aka yi jiya litinin domin tunawa da ranar da aka kaddamar da fafufukar kafa kasar Biafra.

Wasu 'Yan Kabilar Igbo ke fafutikar tabbatar da kasar Biafra domin ballewa daga Najeriya
Wasu 'Yan Kabilar Igbo ke fafutikar tabbatar da kasar Biafra domin ballewa daga Najeriya AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Charlse Muka ya ce jami’an soja sun harbe biyar daga cikin masu fafutukar bayan sun kai hari kan ‘Yan Sanda suka kuma kashe biyu daga cikin su, tare da raunana wasu.

Rahotanni sun ce masu fafutukar sun kuma kai hari kan matafiya a hanyar Asaba zuwa Onitsha.

Amma ‘Yan sanda sun cafke wasu da dama daga cikinsu a Jihohin Enugu da Imo da ke yankin kudu masu gabashi Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.