Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar Kiyaye Haddura a Najeriya ta tura jami'ai 20,000 don taimako lokacin Salla

Hukumar Kiyaye haddura a Nigeria ta tura jamianta akalla dubu ashirin zuwa dukkan hanyoyin kasar domin tabbatar da matuka ababan hawa na tuki da natsuwa yayin hutun sallah da ake cikin yanzu haka.

Shugaban Hukumar kiyaye haddura na farko a Nigeria Wole Soyinka
Shugaban Hukumar kiyaye haddura na farko a Nigeria Wole Soyinka PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Bisi Kazeem kakakin hukumar ya fadawa manema labarai cewa an tanadar da motocin zirga-zirga don gano masu laifi da Babura 283, da motocin jigilan marasa lafiya 76 da motocin janye matattun motoci  daga hanyoyi guda 22.

Kakakin Hukumar kiyaye hadduran na cewa tsakanin watan Janairu zuwa watan Agusta na shekara ta 2015 an sami jimi'llan haddura 5,953 inda mutane 3,233 suka mutu,  amma kuma a bana daga watan Janairu zuwa Agusta mutane 3,048 suka mutu a haddura 5,707 da aka sanar da Hukumar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.