Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya aike wa 'yan Najeriya da sakon salla

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya aike wa al’ummar kasar da sakon murnar sallar layya, in da ya kara tabbatar musu cewa gwamnatinsa, ta dukufa wajen kawo karshen matsin da suka tsinci kansu a ciki. 

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya REUTERS
Talla

Buhari ya ce, tsananin da ake ciki a Najeriya, na da nasaba da tabarbarewar tattalin arzikin duniya da kuma gazawar gwamnatin baya wajen yin kyakkyawan tanadi.

Shugaban ya kara da cewa, kura-kuran da aka yi a can baya, sun shafi yanayin gudanar da rayuwa a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.