Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tsaurara tsaro a arewa maso gabshin Najeriya
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane da dama da rikicin Boko Haram ya dai-daita arewa maso gabashin Najeriya suna koma gidajensu, sakamakon nasarar da sojojin kasar ke yi kan mayakan na Boko Haram.
Wallafawa ranar:
Sai dai kuma Majalisar Dinkin Duniyar ta yi gargadin yiwuwar fuskantar hare-hare jefi-jefi, daga kungiyar ta Boko Haram, da mutanen da ke komawa kauyuka a arewa maso gabashin Najeriyar ka’iya fuskanta, hadi da rashin ababen more rayuwa.
A cewar mai Magana da sashin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinki Duniya Leo Dobbs akwai bukatar ganin an gaggauta sake ginin yankunan da rikicin ya rusa, tare da wadata mutane da abinci domin kaucewa yunwa a yankin.
A baya Majalisar Dinkin Duniyar ta yi gargadin cewa kimanin yara dubu dari biyar ke fuskantar hadarin kamuwa da yunwa a yankin tafkin Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu