Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan sandan Najeriya na gallazawa jama'a

Kungiyar Amnesty International ta zargi wani reshe na rundunar 'yan Sandan Najeriya da ake kira SARS da azabtar da mutane da kuma karbar cin hanci kafin sakin wadanda ake zargi da aikata laifufuka.

Amnesty ta zargi 'yan sandan dake yaki da 'yan fashi da laifin azabtar da jama'a
Amnesty ta zargi 'yan sandan dake yaki da 'yan fashi da laifin azabtar da jama'a Reuters/A.Sotunde
Talla

Kungiyar tayi zargin cewar, mutanen da 'yan sandan dake yaki da 'yan fashi  ya kama na fuskantar azabtarwa, ko horo na rataya, yunwa, ko barazanar harbesu, har sai sun amsa laifin da ake tuhumar su ko kuma su biya makudan kudade kafin a sake su.

Wani matashi mai suna Chidi Oluchi da aka kama a Enugu yace ya sha dan Karen duka kafin ya biya naira 25,500 a sake shi.

Rahoton kungiyar na yau laraba ya biyo bayan bayyanan da tace ta tattara daga mutanen da suka dandana azabar ‘yansandan.

Rundunar 'yan Sandan ta musanta zargin duk da yake tace ba'a rasa bara gurbi a kowanne sashe na al’umma.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.