Isa ga babban shafi
Najeriya

An saki matar Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce 'yan bindigar da suka sace matar Gwamnan Babban Bankin Najeriya sun sake ta tare da sauran mutane hudu da suka sace su tare.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Talla

Mrs Margret Emefiele tana kan hanyarta zuwa kauyensu Agbor da ke jihar Delta, ‘yan bindigar suka taresu tare da sace Mrs Margret, wasu mata guda uku da kuma direbansu.

Jam'ian tsaro sun gano Mrs Margret da sauran mutane hudu a gefen hanyar Benin-Agbor inda da fari 'yan bindigar suka sace su.

Jami'an 'yan sanda suna cigaba da gudanar da bincike a yankin domin gano 'yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.