Isa ga babban shafi
Najeriya

An dakatar da Alkalan da aka zarga da rashin gaskiya

Majalisar Koli ta Shari’a ta Najeriya NJC, ta dauki matakin dakatar da baki dayan Alkalan da ake udanar da bincike kansu bisa zargin aikata cin hanci da rashawa, daga aiki.

Alkalin Alkalan Najeriya, Justice Mahmud Mohammad
Alkalin Alkalan Najeriya, Justice Mahmud Mohammad
Talla

Mukkadashin darakatan yada labaran Majalisar Alkalan, Soji Oye ne ya tabbatar da daukar matakin, a wata sanarwa da ya fitar bayan kammala taronsu a garin Abuja karo na 79.

A baya dai Majalisar ta NJC ta ki amincewa ta dauki matakin dakatar da Alkalan, duk da kiran da kungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta yi na neman a dakatar da su.

A baya Majalisar Shari’ar ta ce dakatar da alkalan ya sabawa sashi na 160 na dokokinta da aka yiwa kwaskwarima a shekara ta 2014.

Wani mataki da Majalisar Alkalan ta kuma dauka, shi ne kafa wani kwamitin tabbatar da da’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa a sashin shari’ar Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.