Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta zabi kashin farko na mutanen da za ta dauka aiki

Fadar gwamnatin Najeriya ta sanar da kammala zabar mutane 200,000 da zata dauka aiki, a matsayin kashi na farko daga cikin 500,000 da ta yi alkawarin dauka a baya.

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Talla

Kakakin mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, Laolu Akande ya sanar da hakan. Ya ce da zarar bankuna sun kammala tantance asusun wadanda aka zaba zasu fara aiki.

Akande ya kara da cewa gwamnatin Najeriya na cigaba da shirye shiryen cika alkawarin daukar sauran mutane 300,000 kamar yadda ta alkawarta.

A cewarsa tantance ma’aikatan kashi na farko, anyi shi ne tsakanin jami’an fadar gwamnatin tarayya da hadin gwiwar ma’aikatun albarkatun Noma da Ma’adanai.

Akande ya ce an zabi kasha 40 daga cikin ma’aikatan ne ta hanyar bawa kowace jiha gurbinta, sai kuma kulawa ta musamman da aka bawa yankin arewa maso gabashin Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.