Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya na zaman makoki

Rundunar sojin Najeriya na zaman makoki saboda rasa wani gwarzon kwamandanta Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, wanda ya rasa ransa tare da wasu jami’ai guda 4 a jihar Borno a fagen yaki da Boko Haram. 

Marigayi Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali da ya rasa ransa a yaki da Boko Haram a jihar Borno da ke Najeriya
Marigayi Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali da ya rasa ransa a yaki da Boko Haram a jihar Borno da ke Najeriya naij.com
Talla

A yau ne ake  gudanar da jana'izar Abu Ali, in da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aike da tawaga karkashin jagorancin babban hafsa Abba Kyari don halartar jana’izar.

Shugaba Buhari ya yaba wa Abu Ali da sauran sojojin da suka riga mu gidan gaskiya a fagen yaki da kungiyar Boko Haram, in da ya ce, ba za a taba mancewa da gudun mawarsu ba.

Tuni dai shugaba Buhari ya kira mahaifin Abu Ali, wato Birgediya Janar Abu Ali mai ritaya ta wayar tarho don yi masa ta'aziyar rashin dansa.

Rahotanni sun ce, Abu Ali  da sauran sojojin guda hudu sun rasa rayukansu ne a kokarinsu na dakile  harin da Boko Haram ta kai a wani barikin soji da ke jihar Borno.

Marigayi Abu Ali ne ya jagoranci kwato akasarin garuruwan jihohin Adamawa da Borno da suka fada hannun kungiyar Boko Haram, dalilin da ya sa shugaban rundunar sojin kasar Janar Yusuf Tukur Burutai ya yi masa karin girma na musamman a shekarar bara.

Margayin ya bar mata da 'ya'ya uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.