"Za'a kammala gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya a sabuwar shekara"
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki, ya ce Majalisar zata kammala gyaran kundin tsarin mulkin kasar cikin watan Janairu na sabuwar shekara.
Wallafawa ranar:
Saraki ya sanar da haka ne, yayin karbar bakuncin shugaban Kungiyar Lauyoyi ta kasa Abubakar Mahmud (SAN).
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce kwaskwarimar kundin tsarin mulkin, ta bawa sashin gyaran fuskar dokokin gudanar da zabukan Najeriya muhimmanci, da suka kunshi, batun dage zabuka bisa dalilan tsaro da kuma inganta tsarin gudanar da kada kuri’a a lokutan zabe.
Karin wasu daga cikin sauran fannonin da za'a yiwa gyara sun hadar da dokokin tafiyar da sashin Shari’ar Najeriya, Ma’aikatar kula da gidajen Yari, da kuma, dokokin tafiyar da hukumomin, yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, da kuma ta yaki da cin hanci da rashawa, ICPC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu