Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta musanta shirin amfani da katin dan kasa a zabukan 2019

Fadar shugaban Najeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bada umurnin amfani da katin shaidar dan kasa domin kada kuri’a zabukan shekara ta 2019.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Talla

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai taimakawa mataimakin shugaban Najeriya kan kankafofin yada labarai Mr Laolu Akande ya fitar.

A cewar Akande, gwamnatin Najeriya tana mutunta hukumar shirya zaben kasar a matsayin mai cin gashin kanta dan haka babu yadda za’ayi ta yi mata katsalandan cikin ayyukanta.

Ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya dai jadda bukatar ganin kowane dan kasa ya mallaki katin shaidarsa ne, kalaman da aka yiwa rashin fahimta a matsayin wanccan umarni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.