'Yar kunar bakin wake mai shekaru 10 a duniya ta kashe kanta a Maiduguri
A tarayyar Nigeriya wata karamar yarinya yar kunar bakin wake mai shekaru 10 ta kashe kanta a wani yinkurin harin da ta kai a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
A cewar shaidu yarinyar ta tarwatsa damarar Bam din dake jikinta ne yan mitoci kafin a isa inda aka yi niyar kai harin.
Nan take dai ta rasa ranta, a yayinda kuma wani mutum guda ya yi mummunan rauni sakamakon tartsatsin fashewar da ta wakana.
yanzu haka dai, jami'an tsaro na ci gaba da gargadin mutane domin su kara lura tare da zura ido kan irin wadannan yan kunar bakin waken, da suka bazu lura da yadda aka tarwatsa sansaninsu dake dajin sambisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu