Isa ga babban shafi
Turkiya

Harin kunar bakin wake ya kashe sojojin Turkiya

Kimanin sojojin Turkiya 13 ne suka gamu da ajlinsu yayin da 48 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka yi amfani da mota makare da bamai-bamai wajen kaddamarwa.

An kai wa sojojin Turkiya hari a barikinsu da ke birnin Kayseri
An kai wa sojojin Turkiya hari a barikinsu da ke birnin Kayseri REUTERS/Murad Sezer
Talla

Gwamnatin Turkiya ta ce, alamu sun nuna cewa, haramtacciyar kungiyar Kurdawa ce ta kai harin a birnin Kayseri, wanda bai fiye fama da tashe-tashen hankula ba.

An dai kai farmnakin ne a dai dai lokacin da sojojin ke shiga motar safa a barikinsu don zuwa cefanan mako.

Wanann na zuwa ne mako guda da aka kai hari makamancin wannan a birnin Santanbul na kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.