Isa ga babban shafi
Turkiya

Harin bam ya hallaka mutane 38 a Istanbul

Mutane 38 sun rasa rayukansu, 30 daga ciki jami'an 'yan sanda, yayinda wasu 166 suka samu raunuka a wani harin bam da akai amfani da mota wajen kai shi, a harabar filin wasan kwallon kafa na babban birnin Turkiya, Istanbul.

Harabar filin wasan kwallon kafa na birnin Istanbul da aka kai harin bam
Harabar filin wasan kwallon kafa na birnin Istanbul da aka kai harin bam REUTERS/Murad Sezer
Talla

Ministan cikin gida na Turkiya Suleyman Soyulu, ya ce an kai harin ne kan wata motar ‘yan sanda jim kadan bayan kammala wasa a filin kwallon kafar, tsakanin kungiyar Burasspor da Besiktas.

A halin yanzu jami’an tsaro sun kama mutane 10, wadanda ake zargi da alaka da kai harin.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai hari. Sai dai a baya sau biyu ‘yan tawayen Kurdawa, suna kai hari a birnin Ankara, yayinda Kungiyar IS ta dauki alhakin harin kunar bakin wake da aka kai birnin na Istanbul har sau 3.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.