Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya musanta karbar na goro daga ENI

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya musanta zargin da ake yi ma sa na karbar na goro daga kamfanonin mai na Shell da kuma ENI bayan sun samu kwangilar Dala bilyan daya da milyan 300 a shekara ta 2011 a Najeriya.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yanzu haka dai wata kotu a birnin Milan na Italiya na gudanar da bincike dangane da wannan zargi, in da aka ce bayan sanya hannu kan wannan kwangila, an bai wa manyan jami’an gwamnatin Najeriya Dala milyan 466, zargin da kakakin Jonathan Ikechukwu Eze ya musanta.

Kazalika zargin ya shafi tsohuwar ministan albarkatun mai na Najeriya, Diezani Alison Madueke.

Sanarwar da kakakin ya fitar ta kara da cewa, babu shakka Mr. Jonathan ya gana da shugabannin manyan kamfanonin mai da ke aiki a Najeriya, in da ya bukace su da su kara kaimi wajen habbaka harkar samar da mai a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.