Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan Sasawa da ke Yobe

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu mahara da ke zaton mayakan Boko Haram ne, sun kai hari kan wani barikin soja dake Sasawa, da ke tazarar kilomita 27 daga garin Damaturu na jihar Yobe, hadi da kona dukiya mai yawa.

Bataliyar Sojin Najeriya da aka kaddamar da ke amfani da babura
Bataliyar Sojin Najeriya da aka kaddamar da ke amfani da babura
Talla

Ko da yake kawo yanzu babu cikakkun bayanan abin da ya biyo bayan harin, kwamishinan `yan sandan jihar ta Yobe, Sumonu Abdulmaliki ya tabbatar da kai harin, sai dai bai yi Karin bayani ba.

Sai dai wata majiya ta ce mayakan sun kone gidaje masu yawan gaske, tare da yin awon gaba da motocin jami`an tsaro uku, sai dai ba`a samu hasarar rayuka ba.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta rawaito cewar, mayakan sun kaddamar da harin ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin, inda suka kutsa kauyen cikin motoci kirar Hilux guda 3 da kuma Babura guda biyu.

Harin na zuwa makwanni hudu bayanda mayakan na Boko Haram suka kai hari kan barikokin soji dake Buniyadi da kuma Kumuya, duka da ke karamar hukumar Gujba a jihar ta Yobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.